Mali da Burkina Faso sun bayyana anniyarsu ta sake karfafa matakan soja kan iyakokinsu kwanaki bayan wani mumunan harin ta'addanci da mayakan jihadi suka kai a Burkina Faso da yayi sanadiyar mutuwar sojoji 24
A yayin da yake ganawa da firaministan Burkina Faso Christophe Dabiré a yammacin jiya, ministan tsaron Mali Janar Ibrahima Dembélé, ya ce tuni bangarorin kasashen biyu suka fara kaddamar da tsaron iyakokinsu na hadin gwiwa, a wani yunkuri na kawo karshen hare-haren ta'addancin da ke addabar kasashen biyu da kuma suka yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.