Kara salwantar rayuka a zanga zangar Sudan | Labarai | DW | 10.01.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kara salwantar rayuka a zanga zangar Sudan

Hashim Abdelrahim da ke magana da yawun 'yan sanda ya ce sun yi nasara ta tarwatsa gangami na masu adawar da gwamnati ta hanyar amfani da hayaki mai sa hawaye.

Masu zanga-zanga uku ne suka rasu bayan da 'yan sanda suka tarwatsa wani gangami na masu gangamin adawa da gwamnati a birnin Omdurman na Sudan kamar yadda 'yan sanda suka bayyana a ranar Alhamis.

A cewar Hashim Abdelrahim da ke magana da yawun 'yan sanda sun yi nasara ta tarwatsa gangami na masu adawar da gwamnati ta hanyar amfani da hayaki mai sa hawaye kasancewar gangamin nasu ya saba wa doka.

A cewar Hashim Abdelrahim dai daga bisani sun samu labari na cewa mutane uku sun rasu yayin da wasu da dama suka samu raunika amma suna ci gaba da bincike. Babu dai cikakken bayani kan yadda mutanen suka rasu cikin jawabin na jami'in 'yan sandan.