Kara kuntatawa ′yan adawa a Masar | Siyasa | DW | 29.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kara kuntatawa 'yan adawa a Masar

Mahukuntan Masar sun kara zafafa matakan da suke dauka a kan kungiyoyi da sauran wadanda ke adawa da mulkinsu, inda suke amfani da alkalan kasar.

A baya bayannan dai mahukuntan na kasar ta Masar sun haramta kungiyar "6 April ta matasa masu fafutuka, wacca ta taka gagarumar rawa wajan kifar da shugaba Husni Mubarak da Mohammad Mursi, a daidai lokacin da kimar sashen shari'ar kasar ke kara zubewa a idanun duniya..

A wani yanayi da ya yi kama da yada kwauron ganga bayan cin moriyarta, kotun tafi da gidanka da sabbin mahukuntan suka kafa, don tinkarar abin da suka kira barazanar ta'addanci da makarkashiyar rugurguza kasa. Kotun ta haramta kungiyar ta 6 April ta matasa masu gwagwarmaya, wacca tuni dama shugabanta, Ahmad Mahir ke zaman yarin shekaru uku, kan laifin yin zanga-zanga ba da izini ba.

Wannan hukuncin da aka yankewa kungiyar ta 6 April, wacca aka kafa ta kusan shekaru bakwai da suka gabata, da zimmar kalubalantar mulkin kama karya da danniya a kasar, hukunci bai yi wa yawancin 'yan kasar ta Masar ba zata ba, musammama bayan yanke makamancinsa ga kungiyar 'yan uwa musulmi, wacca ta yi sama da shekaru 80 tana wanzuwa. Matakin dai ya jawo mai da martini daga masu fafutuka da kuma fashin baki da kwararru.

Imad Gamra, kusa ne a kungiyar ta 6 April, yace wannan hukuncin ba zai sanyasu yin kasa a gwiwa ba, wajan dakatar da fafutukar gyara zama ga shugabancin kasar ba.;

"Wannan hukunci ci-gaba ne na danniyya da kama karya da gwamnatin sojin ina da kisa ke yi, wace take son dinke bakunan masu adawa da ita. Na tabbata, wannan wasan yara da kotun jeka na yika ta yi, bazai kara mana komai ba, face ci gaba da kwarara kan tituna, don mu zama katangar karfe ga irin wadannan hukunce-hukuncen kama karyar"

Sashen shari'ar kasar dai da aka jima anawa kirari da tsimagiyar kan hanya, fyadi yaro fyadi babba, tun bayan kifar da shugaba Mursi kimarsa ke zezayewa a idanun yan kasar dama duniya, musamman bayan da ya wanke illahirin wadanda ake zargi da kashe masu zanga-zangar da ta kai ga kifar da mulkin Husni Mubarak da adadinsu yakai dubu biyu a gefe daya. Kana a daya gefen ya daure hukuncin kisa ga mutane sama da dubu kan laifin kashe dan sanda daya, a yayin da suke taho mu gama da jami'an tsaro, ranar da aka kashe dubban magoya bayan Mursi dake zaman dirshan a dandalin Rabi'atul Adawiyya.

A yayin da yawancin yan kasar da kewa kotunan kasar ke daukar hukunce-hukuncen da wasan yara. Wata tsohowa da aka yankewa danta hukunci, alhali kuma a lokacin baya raye, tun kusan shekaru uku da suka gabata, amma aka yanke masa hukuncin kisa yana kabari abinda ke kara bayyana yadda alkalan jke aiki ba bisa ka'ida ba kuma ba bisa cikakkiyar shaidai ba. inda uwar matashin ta ce.

"Akwai dana da ya jima da mutuwa, amma suka sanya shi cikin wadanda suka yi wa ofishin 'yan sanda kutse.Yayana ba yan kungiyar "Yan uwa musulmi bane, su ko sallama ba sa yi, kai ko hanyar masallacinma basu sani ba"

Sh',aban Maimun, shi ne mutum na hudu cikin jerin wadanda aka yankewa hukuncin kisa a bayan idonsu, ya nuna takaicinsa kan zubewar kimar sashen shari'ar kasar.;

"Dama muna sauraran irin wannan hukuncin daga wannan alkalin dake aikin hauni. Abin da yafi kona min zuciya shine, yadda sashen shari'ar Masar baya zama abin dariya a duniya. Ayanzu babu gwamnti ko doka a Masar"

Mawallafi: Mahmud Yaya Azare

Edita: Usman Shehu Usman.

Sauti da bidiyo akan labarin