Kano: Martani kan nada shugaban sarakuna | Siyasa | DW | 09.12.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kano: Martani kan nada shugaban sarakuna

Bayan kammala dambarwar tabbatar da dokar karin masarautu 4 a Kano, yanzu an shiga matakin yin amfani da sashin wannan doka da ya bai wa gwamna damar nada wanda zai fara shugabantar majalisar sarakunan.

Nadin da aka yi wa sarki Muhammad Sunusi na 2 a matsayin shugaban majalisar na farko ya jawo kace-nace a tsakanin mutane inda galiban ake ganin kamar wani shiri ne na karasa raba shi da kujerar mulkin.

Da fari dai an yi ta yada jita jitar cewar sarkin Bichi Aminu Ado Bayero shi za a nada a matsayin shugaban majalisar sarakunan na farko, amma sanarwar da gwamnatin Kano ta fitar a wannan Lahadi wacce ta ayyana sarkin Kano Muhammad Sunusi na 2 a matsayin shugaban wannan majalisa ta farko ya rufe wancan babin.

Batun Aminu Ado Bayero sai dai ya bude sabon shafin kace nace in da wasu ke ganin cewar nadin da aka yi wa Muhammad Sunusin tamkar tarko aka kafa masa domin samun sada laifin da ka iya bayar da damar cire shi, ko kuma rage masa mukami kamar yadda dokar ta baiwa gwamna dama.

Nigeria Wahlkampf von APC-Partei in Kano

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje

Sai dai kuma makusantan gwamna Abdullahi Umar Ganduje irinsu Auwal Lawal Aronposu na cewar gwamna ya yi wannan nadi da kyakyawar manufa amma batun karba karba yana nan bayan shekara 2.

Sharu Mustapha Naburuska kuwa a ra'ayinsa cewa ya yi ko kadan bai kamata Sarki Muhd Sunusi ya karbi wannan mukami ba, domin wata kutungwila ce kawai aka saito masa domin dora shi a kan keken bera.

To kamar yadda wasu ke zargi dai wannan mukami tamkar yunkuri ne na shirya wa sarki Muhd Sunusi na 2 wata kutungwila, amma Dalhatu Isa lauya mai zaman kansa a Kano ya ce ba haka ba ne. Kuma batun kara da take a gaban Justice AT Badamasi wacce masu nada sarakuna suka shgar ba zata hana sarki bin wannan doka ba.

 

Sauti da bidiyo akan labarin