1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sheikh Abduljabbar zai fuskanci hukunci

Nasir Salisu Zango BAZ/LMJ
December 15, 2022

Wata kotun shari'ar Musulum ci a jihar Kanon da ke Najeriya, ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara kan samunsa da ta ce ta yi da laifin batanci ga Annabi Muhammad.

https://p.dw.com/p/4KywJ
Nigeria | Abduljabbar Nasiru Kabara | Kleriker
Hoto: Aliyu Samba

Mai shari'a Ustaz Ibrahim Sarki Yola ya ce kotu ta tabbatar da cewar kalaman batanci da Malam Abduljabbar ya yi ga Annabi cikin karatunsa, shi ne ya kirkire su domin shaidu da hujjoji sun tabbatar babu su a cikin litattafan da yake fada. A sabo da haka kotun ta ce ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya, ta kuma byar da umurnin kwace Masallatansa guda biyu da littattafai mallakar malamin. Kotun ta ce ta yanke wannan hukunci ne karkashin sashe na 382 na kundin Penal Code. Tuni dai almajiran malamin da ya ce ba ya neman afuwa kuma yana son a gaggauta zartas masa da hukuncin,  suka ce ba su yi mamakin hukuncin kisa ta hanyar ratayar da aka yanke masa ba. A cewar su da ma sun san an gama shirya yi masa wannan hukunci, a hannu guda kuma jami'an tsaro a Kanon sun ci gaba da zama cikin shiri domin dakile duk wani tashin hankali ko tarzoma daga almajiran malamin.