Kanada za ta soma kwasar ′yan gudun hijira na Siriya | Labarai | DW | 10.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kanada za ta soma kwasar 'yan gudun hijira na Siriya

A wannan Alhamis din ce jirgin dauke da 'yan gudun hijirar kasar Siriya 300 zai sauka a birnin Toronto na kasar Kanada a cewar Firaministan kasar Justin Trudeau.

Jirgi na biyu na sojan kasar ta Kanada da ke dauko 'yan gudun hijirar na Siriya daga Jordan, zai tashi ne a ranar Asabar mai zuwa wanda shi kuma zai sauka a birnin Montreal. Kasar ta Kanada dai ta tanada wadannan filaye jiragen kasar guda biyu na Toronto na da birnin Montreal a matsasyin mashigar 'yan gudun hijirar, inda bayan an yi musu gwaje-gwaje a fannin kiwo lafiya, za'a rarraba su sannu a hankali cikin biranen kasar 36.

Hakan dai na daga cikin tsarin kasar ta Kanada na daukan 'yan gudun hijirar dubu 10 nan zuwa karshen wannan shekara, sannan kuma wasu dubu 15 a sabuwar shekara mai kamawa ta 2016. Tun dai daga watan Janeru na bara, kasar ta Kanada ta karbi 'yan gudun hijira 3.500.