Kanada za ta mika maganin cutar Ebola ga WHO | Labarai | DW | 13.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kanada za ta mika maganin cutar Ebola ga WHO

Kanada ta ce za ta baiwa Kungiyar Lafiya ta Duniya WHO maganin gwaji na cutar nan ta Ebola da yanzu haka ta hallaka mutane da dama a kasashen da ke yammacin Afirka.

Mukaddashin shugaban hukumar kula da lafiyar al'umma ta Kanada ne ya bayyana hakan a jiya Talata, inda ya kara da cewar nan gaba kadan za a mikawa Kungiyar ta Lafiya magunguna kimanin 800 zuwa 1000.

Tuni da jami'an bada agaji na kiwon lafiya na Medecins Sans Frontieres suka yi na'am da wannan mataki wanda ke zuwa 'yan sa'o'i kalilan bayan da Kungiyar Lafiya ta Duniya ta ce za a iya amfani da maganin na gwaji kan bil adama.

To sai dai duk da wannan, kungiyar ta ce maganin kadai ba zai dakile yaduwar cutar ba inda ta ke cewar dole ne a kara yawan jami'an kiwon lafiya da za su kula da wanda suka kamu da cutar.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu