1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Kanada ta janye halascin shan miyagun kwayoyi

April 27, 2024

Kanada ta janye dokar da ta ayyana a shekara a 2023 na bawa al'umma damar ta'ammali da miyagun kwayoyi da bai wuce nauyin gram 2.5 a bainar jama'a ba, hukumomi sun ce hakan na shafar lafiyar al'umma.

https://p.dw.com/p/4fFQN
Wani 'dan kwaya da ke zaune a yankin British Columbia da ke kasar Canada
Wani 'dan kwaya da ke zaune a yankin British Columbia da ke kasar CanadaHoto: David Tesinsky/ZUMAPRESS.com/picture alliance

Gwamnatin lardin British Columbia ita ce ta dakatar da dokar kamar yadda Firimiyan yankin David Eby, ya sanar a shafinsa na X,  ya ce jami'an 'yan sanda zasu ci gaba da aikin kakkabe masu ta'ammali da kwayoyin a wuraren taruwar jama'a ciki har da asibitoci da wuraren cin abin abinci da bakin ruwa harma da wuraren shakatawar jama'a.

Karin bayani: Mutum na karshe na harin Kanada ya mutu

Firimiyan ya kara da cewa wannan mataki ya kawo karshen dokar da ake ta cece-kuce a kai daga ciki da wajen kasar, wanda tun da fari ta bawa al'umma damar amfani da miyagun kwayoyin a bainar jama'a da suka hadar da hodar iblis da heroin da dai sauransu.

Karin bayani: Kanada ta hana 'yan Afirka zuwa taron HIV/AIDS a kasarta

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da Mataimakiyar kwamishiniyar 'yan sandan Vancouver, Fiona Wilson, ta bayyana wa zauren majalisar dokoki cewa 'yan sanda basu da hurumin hana mutane shan kwaya, matsala ce da ta shafi bangaren kiwon lafiya da hukumomi ya kamata su tashi tsaye.