1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin tallafawa 'yan gudun hijira

May 16, 2019

Wasu hamshakan kamfanoni da manyan ‘yan kasuwa a Najeriya da hadin guiwar MDD sun kaddamar da wani shiri na tallafawa mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya.

https://p.dw.com/p/3Ib5z
Nigeria Flüchtlingslager Flüchtlinge Kinder
Hoto: DW/S. Ciochina

Saboda karfafa ayyukan jin kai musamman a shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya wanda rikicin Boko Haram ya daidaita manyan kamfanonin da ‘yan kasuwa a Najeriya su ka fito da shiri da za su yi aiki da majalisar dinkin duniya domin bada tasu gudumowa daga irin ribar da su ke samu don ragewa ‘yan gudun hijira halin ni ‘ya su da su ke ciki.

Wannan shiri wanda shi ne irin na farko a duniya da kamfanonin masu zaman kan su gami da manyan ‘yan kasuwa za su hadu na da zummar samar da kimanin dalar Amurka miliyan 80 ko kuma Naira biliyan 30 domin tallafawa aikin jin kai a wannan sashi na Najeriya.

Tawagar shugabannin kamfanonin da ‘yan kasuwa tare da jami'an majalisar dinkin duniya sun ziyarci Maiduguri inda su ka je su ka ga ‘yan gudun hijira domin sanin halin da su ke ciki da kuma duba hanyoyin da za abi domin magance musu matsalolin da su ke ciki.

Bayan duba halin da ‘yan gudun hijira ke ciki tawagar ‘yan ksuwa da shugabannin kamfanonin sun gana da manema labarai tare da bayyana musu musabbabin wannan mataki da su ka dauka kamar yada Wale Tinubu ya bayyana.

'Yan gudun hijirar Boko Haram a Maiduguri
'Yan gudun hijirar Boko Haram a MaiduguriHoto: picture-alliance/dpa/EPA/Stringer

 "Mun fadawa kan mu cewa in kaashe da wannan kalubale na jin kai bai shafe su ba su ka tara makudan kudade domin tallafawa mutanen mu mafi karancin abinda za mu yi shi ne rubanya kokarin mu domin yin abinda ya fi wanda sauran kasashen duniya su ka yi. Za mu tara kudi Naira biliyan 30 ko kuma Dalar Amurka miliyan 80 da manyan mutane da su ka kudiri aniya za mu samu nasarar kan abinda mua sa a gaba”

Ganin wannan shi ne karo na farko da ‘yam kasuwa gami da manyan kamfanonin su ka hada kai domin samar kudi domin aikin jin kai majalisar dinkin duniya ta yi imanin za a samu kudaden d za a maganace matsalolin ‘yan gudun hijirar kamar yadda Edward Kallon jami'in kula da ayyukan jin kai na majalisar ya bayyana.

"Duk inda ka samu masu hannu da shuni wadan su ka fahici girman matsalar za su bada kudaden da ake bukata. Akwai kudi a duniyan nan da za a iya magance kowace irin matsala sai dai su na hannun mutane kalilan ne, sai dole mun gamsar da su bukatar fitar da kudi don taimakawa mabukata”

Mata 'yan gudun hijira
Mata 'yan gudun hijiraHoto: picture-alliance/dpa/EPA/Stringer

Bisa hasashen samun asarar shirin ne gwamman jihar Borno Kashim Shetima ya nemi wannan shiri ya da taimaka wajen bunkasa ilimi a jihar wanda ke zama sahun baya tsaknain takwarorin ta.

"Zan roke ku ku taimakawa fannin bunkasa ilimin mu da yanzu haka muke maida hankali aka inda muka gina manyan makarantu don farfado da ilimi. Yanzu haka muna da marayu sama da dubu 50 da kuma mata da su ka rasa majen su wanda in ba mu kula da su a annan lokaci ba nan da shekaru 10 zuwa 15 su zasu kula mu da irin hanyarsu”

An yi imanin wannan shiri in aka bi shi sau da kafa zai samu nasarar da ake bukata kuma tuni da yawa daga cikin ‘yan gudun hijira su ka yi maraba da shirin da su ke ganin irin sa ne kawia zai cire musu kitse a wuta.