Kamfanin Facebook ya samar da manhajar hana magudi | Labarai | DW | 28.01.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kamfanin Facebook ya samar da manhajar hana magudi

Kamfanin Facebook ya samar da wasu sabbin manhajoji da ka iya taimakawa wajen hana aiwatar da magudin zabe ta yanar gizo.

Kamfanin ya yi hakan ne don kawar da duk wani yunkuri na yin katsalandan a harkokin zabe musanman na nahiyar Turai.Manhajoji za su tabbatar da adalci na yadda ake talata 'yan takara ba tare da nuna bangaranci ba. Wannan ya biyo bayan zargin kamfanin na bai wa wasu hade-haden manhajoji, bayanan masu anfani da shafukan na facebook inda suke hana wasu.