1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamfanin Facebook ya nemi afuwar duniya

Binta Aliyu Zurmi MAB
October 5, 2021

Bayan matsalar katsewar sadarwa da kamfanin Facebook ya fuskanta a jiya, shugaban kanfanin Mark Zuckerberg ya ba wa ma'abota shafukan sada zumunta hakuri bayan da komai ya daidaita.

https://p.dw.com/p/41GSS
Störung | WhatsApp, Facebook und Instagram
Hoto: Revierfoto/dpa/picture alliance

Kamfanin sadarwa na Facebook da Instagram gami da WhatsApp bayan daukewar sadarwa na 'yan wasu sa'o'i a jiya Litinin, shugaban kamfanin Mark Zuckerberg ya nemi afuwar al'ummar duniya sakamakon tsaikon da hakan ya janyo ga al'amuransu na yau da kullum.

Kamfanin ya shaida matsalar ta auku ne sakamakon inganta wani bangare na kamfanin, wanda ya kai ga garin gyaran gira aka rasa ido. Sama da mutum biliyan uku ne suka kasa shiga shafukansu, wanda hakan ya janyo wa masu masasanantu dimbin asara, ko a na su bangaren masu hasashe na ganin kamfani shi ma ya tafka dimbin asarar miliyoyin kudi na dalar Amirka.


Wannan matsalar dai na zuwa ne a daidai lokacin da wata tsohuwar ma'ikaciyar kamafanin ta fallasa yadda kamfanin ke maida fifiko a kan kudaden da yake samu maimakon kan yadda mutane musamman ma matasa ke bata lokaci a shafukan sadarwar kamfanin.