Kamen ′yan jarida ya karu a shekara ta 2016 | Labarai | DW | 13.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kamen 'yan jarida ya karu a shekara ta 2016

Kungiyar kare hakkin jarida ta kasa da kasa ta Reporteur Sans Frontiere ta ce adadin 'yan jarida da aka kama ko kuma ake tsare da su a kasashen duniya daban-daban ya kai 348 a shekarar 2016. 

Kungiyar ta bayyana haka ne a cikin rahoton bitar aikin jarida na shekara da ta fitar a wannan Talata inda ta ce ya zuwa yau 'yan jarida 348 ne ake tsare da su a gidajan kurkuku a fadin duniya. 

Kungiyar ta Reporteur Sans Frontiere wato RSF a takaice, ta kara da cewa adadin 'yan jaridar da ake tsare da su ya karu da kashi 22 cikin 100, ya kuma nunka har sau hudu a kasar Turkiyya, inda ake tsare da 'yan jarida sama da 100 bayan yinkurin juyin mulkin da aka yi a kasar da ya ci tura. 

Rahoton ya bayyana cewa adadin 'yan jarida mata da aka tsare ya nunka gida hudu a shekarar bana inda yanzu haka ake tsare da mata 'yan jarida 21 sabanin biyar kawai a shekarar da ta gabata.