1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ruwanda: Kama fitaccen dan adawa

Mouhamadou Awal Balarabe LMJ
September 2, 2020

'Yan sandan Ruwanda na ci gaba da tsare shahararren dan adawan kasar Paul Rusesabagina bisa zargin kitsa ayyukan ta'addanci a shekarun baya.

https://p.dw.com/p/3hugh
Ruanda Paul Rusesabagina
Shahararren dan adawar kasar Ruwanda da aka kama Paul RusesabaginaHoto: Imago Images/Belga/M. Maeterlinck

Hukumomin Ruwanda sun jima suna neman Paul Rusesabagina ruwa a jallo, amma kariya da yake samu a kasar Beljiyam ta sa aka kasa kama shi saboda yana rike da fasfo din kasar. Sai dai kuma sammacin kasa da kasa da fadar mulki ta Kigali ta fitar, ya sa ta samu hadin kan wasu kasashen duniya wajen cimma burinta. Ita dai gwamnatin Ruwanda ta zargi Rusesabagina da taka rawa wajen neman hambarar da Shugaba Paul Kagame da kuma kafa kungiyoyin 'yan ta'adda a yankin tafkunan Afirka.

 

Karin Bayani: Sharhi: Nasarar Kagame ba ta zo da mamaki ba

 

Masu bincike na Ruwandan sun ce Rusesabagina na da hannu a satar mutane da kisan kai da haddasa gobara. Alal hakika ma dai sun ki yin bayani a kan hanyoyin da aka bi wajen damke shi, saboda a cewarsu zai iya kawo cikas ga binciken da ake gudanarwa. sai dai iyali da dangin dan hamayyar da aka daure tun ranar Litinin, sun ce an sace shi ne a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa. Ita kuwa kasarsa ta biyu wato Beljiyam, ta ce ba ta da masaniya ko hannu a kamen nasa.
Shi ma tsohon firaministan Ruwandan Faustin Twagiramungu mai adawa da gwamnatin Kigali, ya yi tir da abin da ya faru: "A gare mu ba ma kame ba ne wannan, sace shi aka yi  bisa hadin bakin hukumomin wasu kasashe. Paul Rusesabagina dan asalin kasar Beljiyam ne a yanzu kuma yana rike da katin zama a kasar Amirka. Me ya sa gwamnatin Rwanda ba ta nemi gwamnatin Beljiyam ko ta Amirka ta aika mata da shi ba?''

Faustin Twagiramungu ehemaliger Premierminster von Ruanda
Tsohon firaministan Ruwanda Faustin TwagiramunguHoto: Getty Images/AFP/G. Gaudin

 

Karin Bayani: An yanke hukuncin kaso ga shugabannin FDLR

 

Paul Rusesabagina wanda dan kabilar Hutu ne, ya taba zama daraktan Hôtel des Mille Collines a Kigali, yayin kisan kare dangi wanda ya yi sanadiyyar mutuwar kusan mutane dubu 800,000 galibi tsirarun kabilar Tutsi a tsakanin watan Afrilu zuwa Yulin 1994.  Wasu 'yan Ruwanda na ganinsa a matsayin jarumi wanda ya ceci rayukan mutane sama da 1,000 ta hanyar ba su mafaka a otal din, amma wasu daga cikin manyan jami'an gwamnatin Paul Kagame suna kiransa da mayaudari. Wannan kuwa ba ya rasa nasaba da suka da yake yi ga lamirin gwamnatin ta Kagame wanda kungiyar ta FDR take da hannu dumu-dumu a zubar da jinin da aka yi.

DR Kongo Beerdigung von Etienne Tshisekedi
Shugaba Paul Kagame na RuwandaHoto: Presidence RDC

A lokacin da yake gudun hijira, Rusesabagina ya kafa jam'iyyar MRCD. Amma Thierry murangira kakakin hukumar binciken ta Rwanda, ya ce sun bi hanyoyin da suka dace wajen kama dan siyasar: "Ya dade sosai da aka fitar da sammacin kame Rusesabagina domin ya fuskanci tuhume-tuhume kamar ta'addanci da barna da satar mutane da kisan kai da ake masa. Wadannan laifukan an aikata su a kan fararen hula. Kotu za ta ci gaba da neman wadanda suka boye. Muna da karfi da niyya, batu ne kawai na lokaci. "

Rusesabagina dai ba shi ne dan adawa na farko da aka kama a kaetare kuma aka tasa keyarsa zuwa Ruwanda ba, sai dai kama fitaccen dan siyasar na iya haifar da rarrabuwar kawuna tsakanin shugabannin yankin, a cewar Kassim Kayira mai sharhi kan harkokin siyasa da ke da zama a birnin London na kasar Birtaniya. 

Shugaba Kagame wanda  ya shekara 20 a mulkin Ruwanda  ya dare kan kujerar mulkin kasar ne a 1994, yana shan suka game da salon shugabancinsa na ba-sani-ba-sabo, tare da danne duk wani nau'i na adawa da daure wadanda ra'ayin siyasarsu ya sha bamban. Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta zargi gwamnatin Kagame da kisan gilla da kame da tsare mutane ba bisa ka'ida ba tare da azabtar da abokan hamayya.