1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Murna ta koma ciki tsakanin fasinsojin wani jirgin ruwa

Zulaiha Abubakar
February 18, 2020

Murna ta koma ciki tsakanin fasinsojin nan da suka dauki kwanaki a cikin jirgin ruwa a kasar Kambodiya, yanzu haka dai matafiyan na zaman wucin gadi a wani Otel na kasar sakamakon rashin amincewar kasashe makwabta.

https://p.dw.com/p/3XxtD
Kambodscha Kreuzfahrtschiff Westerdam eingetroffen
Hoto: AFP/Tang Chhin Sothy

Sakamakon gwajin lafiyar matafyan da yawansu ya kusan 2,000 ya tabbatar da samun mutum guda dauke da kwayar cutar yayinda sauran fasinjojin suke cikin koshin lafiya, kodayake kasashe makota sun bayyana fargabar  billar cutar ta Coronavirus idan matafiyan sun koma muhallansu,

Tashoshin ruwa biyar ne dai suka haramtawa jirgin ruwan sauke matafiyan a wanann wata tun bayan mutuwar daruruwan mutane a Chaina.