1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan aware sun tsare hanyar shiga ko fita daga Bamenda

Ramatu Garba Baba
September 9, 2018

An zargi mayakan sa kai na yankin da ke fafutukar ballewa a kasar Kamaru da laifin tayar da rikici bayan da suka tsare hanyar shiga ko fita daga yankin Bamenda.

https://p.dw.com/p/34aS4
Kamerun - Proteste
Hoto: Getty Images/AFP/Stringer

Mayakan sun farfasa duk motocin fasinjojin da suka tare, inda direba guda ya rasa ransa a sakamakon hatsaniyar. Mayakan sun ce, sun dauki wannan mataki a matsayin gargadi ga gwamnatin shugaba Paul Biya, da ta kaucewa gudanar da zabe a yankin da suka ce na zama ne a matsayin kasa mai cin gashin kanta. Wani babban jami'in sojan kasar mai suna janar Agha Robinson, ya tabbatar da labarin sai dai ya ce an shirya daukar matakin shawo kan lamarin tare da kwace makamai daga hannun mutanen da ya kira 'yan ta'adda.

Rikicin son ballewar yankin na Ambazoniya ya soma ne a shekarar 2016 bayan da lauyoyi da malamai suka nuna adawa kan tilasta musu yin amfani da Faransanci a yankin da aka fi anfani da turancin Ingilishi, kuma mutum dari uku ne suka mutu yayin da dubbai suka tsere daga gidajensu a sanadiyar tashe-tashen hankula, lamarin da yanzu ya kasance babban kalubale a zaben shugaban kasa da ke karatowa.