Kamaru: Wani shugaban gunduma ya bace | Labarai | DW | 12.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kamaru: Wani shugaban gunduma ya bace

Bikin ranar matasan Kamaru na wannan shekarar ya gudana cikin yanayi na rudani bayan da aka samu labarin kashe wasu Jandarmomin kasar guda uku da kuma bacewar wani shugaban gunduma a yankin Batibo.

An kashe Jandarmomin uku ne a garin Kembon a yankin Kudu maso yammacin kasar, inda aka samu wasu hare-hare nan da can kafin a shayo kan matsalar a cewar Kanal Didier Badjeck mai magana da yawun rundinar sojojin kasar ta Kamaru. A yankin Batibo kuwa da ke Arewa maso yammacin kasar inda ake magana da turancin Ingilishi, an tarar da motar shugaban gundumar Namata Dientg a kone kurmus, sai dai kuma shi ba'a san inda ya shiga ba har ya zuwa yammacin ranar Lahadi a cewar dan majalisar yankin na Batibo Joseph Mbah-Ndam. Tun farkon rikicin yankin da ake magana da turancin Ingilishi a Kamaru a shekara ta 2016 kawo yanzu, an samu rasuwar jami'an tsaro 26 kaman yadda gwamnatin kasar ta sanar.