Kamaru ta tabbatar da mutuwar mutane 25 a kurkuku | Labarai | DW | 14.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kamaru ta tabbatar da mutuwar mutane 25 a kurkuku

Ministan sadarwa na kasar Kamaru Issa Tchiroma Bakary ya ce mutanen 25 na daga cikin 56 da aka cafke ne bisa zarginsu da kasancewa 'ya'yan kungiyar Boko Haram.

Sai dai kakakin gwamnatin ta Kamaru ya musanta zargin da ake yi wa rundunar sojojin kasar na cin zarafin jama'a, da sunan farautar mayakan tada kayar baya. An tarar da gawarwakin mutanen 25 ne, yini guda bayan an cafkesu a watan Disamban da ya gabata, a cewar ministan sadarwa na Kamaru Issa Tchiroma Bakary, a taronsa da manema labaru. Kuma su na daga cikin mutane 56 da aka tsare ne, amma ana kan gudanar da bincike dangane da mutuwar ta su.

Ya ce har yanzu dai babu wani sakamako da ke alakanta mutuwar tasu da kisan da gangan a bangaren jami'an tsaron kasar. A cewar Tchiroma Bakary, an sauke wani babban jami'in sojin daga mukaminsa, sakamakon wannan bincike da ake ci gaba da yi.

A watan Janairu ne dai gamayyar masu fafutukar kare hakkin jama'a a tsakiyar Afrika, dake da matsuguni a Yahounde, ta ce majiya mai tushe ya tabbatar da kisan gilla wa wasu mutane 50 da aka kulle bisa zarginsu da zama 'yan Boko Haram, daga bisani aka binne su a rami guda.