Kamaru ta fitar da sabbin dabarun kyautata muhalli | Zamantakewa | DW | 06.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Kamaru ta fitar da sabbin dabarun kyautata muhalli

Bisa la'akari da karuwar barazanar sauyin yanayi da irin illolin da ya kan janyo ga muhalli, Kamaru ta dauki wasu matakan rigafi musamman wajen gudanar da ayyukan ci gaba

Kwararrun masu nazarin muhalli daga manyan jami'o'i na duniya sun yi ittifakin cewa barazanar sauyin yanayi na iya shafar rayuwar al'umomi da dabbobi game da tsirrai da ke nahiyar Afirka. Kwararrun sun bayyana hakan ne a wani nazarin yanayin muhalli da suka yi na kasar Kamaru.

Yadda ake sare bishiyoyi kenan a dajin Lom Pangar da ke gabashin kasar Kamaru da niyyar kafa tashar wutar lantarkin da zai iya samar da akalla megawatt 30. A kusa da wajen kuwa, akwai bututun mai da suka hada kasar daga Chadi duk dai karkashin wannan dajin da ake batu a kansa.

Aikin gina tashar wutar dai Bankin Duniya ne ke yin sa kan kudi dalar Amurka miliyan 132, daya daga cikin ayyukan da mataimakin shugaban bankin Mukhtar Diop ya kuma ziyarta.

'' Muna da aikace-aikace da yawa da suka zarta na dala biliyan guda a halin yanzu, kuma kaso mafi yawa daga cikin rabe-raben ayyukan dake a nahiyar Afirka, suna cikin Kamaru ne, abin da kenan ke nuna kyawun dangantakar bankin duniya da kasar''

Lom Pangar Damm

Dam din Lom Pangar wanda ake sa ran zai kara yawan wutar lantarki a kasar

Sai dai fa kwararru kan nazarin muhalli na ganin irin wadannan ayyuka duk da yake suna da amfani ta fuskar tattalin arziki, akwai su da lahanta muhalli kwarai da gaske, musamman a kasashen Afirka, kamar dai yadda shima aikin samar da katako ga kasashe manya irin su China da Turai dama yankin Amurka.

Thomas Smith wani kwararren mai nazarin yanayin muhallin Afirka ne daga Jami'ar California ta Amurka, ya kuma ce karuwar dumamar yanayi da sare-saren itatuwa ke haddasawa na iya ci gaba da batar da dabbobin dawa suma, saboda shafar muhalli nasu.

''Idan aka yi la'akari da karuwar yanayi na zafi da makin digiri 1.5 a duniya, nahiyar Afirka na iya asarar kashi 30 cikin dari na dabbobi da kuma tsirran ta babu ma kamar bishiyoyi. Haka akwai batun karuwar sinadarin Carbon dioxide da kashi 3 a duniya yanzu, wannan ma na iya shafar akalla kashi 40 cikin dari na dukkanin dabbobin dake a Afirkan nan da karshen karnin da ake ciki''

Mawallafi: Muntaqa Ahiwa
Edita: Pinado Abdu Waba