1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru: Soji sun kashe farar hula a Buea

Gazali Abdou Tasawa
September 24, 2018

A Kamaru jami'an tsaro sun bindige wasu fararan hula biyu a wannan Litinin a birnin Buea na yankin Kudu maso yammacin kasar da ke zama daya daga cikin yankunan da ke fama da tayar da kayar bayan 'yan awaren Ambazoniya.

https://p.dw.com/p/35Q5V
Kamerun Sprachenstreit Englisch
Hoto: Getty Images/AFP

Kamfanin dillancin labaran Faransa wanda ya ruwaito labarin ya bayyana cewa shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa mutanen biyu daya duroban tasi daya kuma mai shago na tsaye a bakin titin unguwar Molyko da ke zama unguwar daliban birnin na Buea lokacin da sojojin suka bude masu wuta. 

Yanzu haka dai hotuna da bidiyon gawarwakin mutanen biyu a yashe na ta yawo a shafukan saka zumunta. Harakokin tsaro dai na ci gaba da tabarbarewa a yankin masu amfani da Turancin Inglishin a dai dai loakcin da zaben shugaban kasar na ranar bakwai ga watan Oktoba ke kara karatowa a kasar ta Kamaru.