Kamaru: Kotu ta wanke Ahmed Abba na RFI | Labarai | DW | 21.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kamaru: Kotu ta wanke Ahmed Abba na RFI

Kotun sojojin Kamaru ta wanke a Ahmed Abba dan jaridar nan wakilin sashen Hausa na gidan rediyon Faransa na RFI a kasar, daga babban zargin da ake yi masa na halasta kudaden haram da kuma gudanar da ayyukan ta'addanci. 

Kotin ta bayyana wannan hukunci ne a zaman da ta yi kan daukaka karan da dan jaridar ya yi a gabanta kan hukuncin farko na zaman wakafi na shekaru 10 da tarar kudin Euro dubu 85 da ta yanke masa a shekara ta 2016. Sai dai kuma bayan da ta wanke shi daga laifin farko kotun ta yanke masa hukuncin zaman kaso na watanni 24 a bisa samunsa da laifin boye asirin ayyyukan ta'addancin da ya ke da masaniya a kansu. A watan Yulin 2015 ne dai mahukuntan kasar ta Kamaru suka kama dan jaridar a birnin Maroua na arewacin kasar inda ya je aiko da rahotanni kan rikicin Boko Haram.