Kamaru : Gwamnati na neman sulhu da ′yan aware | Siyasa | DW | 12.09.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kamaru : Gwamnati na neman sulhu da 'yan aware

Tun kimanin shekaru uku da suka gabata ake fama da tashin hankalin na Kamaru wanda ake ganin Shugaba Paul Biya ya yi sako-sako amma yanzu ya yi alkawarin shirya wani taron tattaunawa na kasa.

Bisa al'ada dai sau uku a shekara Shugaban Kasar Kamaru Paul Biya yake jawabi ga 'yan kasar. Amma rikicin da aka kwashe tsawon shekaru uku ana yi da 'yan aware a yankunan masu amfani da harshen Ingilishi ya sa shugaban ya sanar da cewar za a gudanar da babban taron tattaunawa domin samun bakin zaren warware rikicin a karshen wannan wata na Satumba. Sai dai an samu martani mabambamta kan jawabin na Shugaba Biya. Simon Ntonga mai nazarin harkokin siyasa ne  a Kasar ta Kamaru da ya yi fatan cewa shugaban zai cika alkawarin da ya dauka. Ya ce: "A karon farko ina iya cewa mun gano cewa da gaske shugaban kasar yake a kan abin da ya fada da kuma yake tunani, zai tabbatar da dukkan alkawuran da ya yi a cikin sanarwar." 

 

Sauti da bidiyo akan labarin