Kamaru: Cece-kuce kan yi wa majalisar ministoci garambawul | BATUTUWA | DW | 05.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Kamaru: Cece-kuce kan yi wa majalisar ministoci garambawul

Shugaba Paul Biya ya yi garambawul a majalisar ministocinsa amman duk da haka ana ganin tsugune ba ta kare ba, a yayin da 'yan yankin da ke amfani da harshen Ingilishi ke danganta nade-naden da na ran sarki ya dade.

Garambawul na gwamnatin Kamaru ya shafi ministoci da dama, amma kuma hankali ya fi raja'a kan ministocin cikin gida da na matakin ilimin sakandare, saboda wannan shi ne karon farko da aka mika mukaman ga 'yan bangaren Ingilishi. Sannan kuma shi sabon ministan ciki gida Paul Atanga Nji yana sahun wadanda suka karyata labarin tada kayar baya lokacin da 'yan yakin Ingilishi suka fara zargin mayar da su saniyar ware. Saboda haka ne 'yan yankin Ingilishi ke ganin cewar matar jiya bata canza zani ba, saboda 'yan amshin shatar gwamnati aka nada. Garba Umaru Nalado, Sakataren tsare-tsare na Jam'iyyar SDF mai adawa kuma dan asalin yankin da ke magana da Ingilishi na Kamaru na daya daga cikin masu wannan ra'ayi.

Shugaba Paul Biya ya kafa masana'anta ta musamman da za ta kula da raya yankuna 10 da ake da su a Kamaru, tare da sa ido kan shirin sakar wa kananan hukumomi mara. Lamarin da ka iya dace wa da bukatar 'yan yankin Ingilishi da ke neman a dawo da tsarin tarayya da kamaru ta yi amfani da shi a baya don su ci gajiyar arzikin da Allah ya hore wa yankinsu. Mouhamadou Yakoubou, mataimakin magajin garin birnin Douala ya ce wannan mataki na kafa sabuwar ma'aikata ya nunar da cewar Paul ya duba koke-koken Anglophone da idanun basira.

Sai dai kuma nada Nalova Lyongha Pauline Egbe tsohuwar shugabar jami'ar Buea (Boya) a matsayin ministar matakin ilimi na sakandare ya bar baya da kura. Wasu na ganin cewar za ta taka rawar wajen inganta tsarin ilimi na Ingilishi domin ya yi daidai da tsarin Faransaci na kamaru. Amma Garba Umaru Nalado ya ce koma-baya za ta jawo idan aka yi la'akari da kamun ludayinta a jami'a.

Abin da aka fi sa ido ya kai shi ne wanda zai rike mukamin shugaban majalisar dattawa na Kamaru bayan zaben 25 ga wannan wata na Maris, don a sani ko an fara rabon mukamai daidai wa daida tsakanin masu amfani da Faransanci da kuma masu amfani da Ingilishi, kasance shugaban kasa da kakakin majalisa da shugaban majalisar dattawa na Kamaru na hannun Francophone a yanzu.

Sauti da bidiyo akan labarin