1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MSF ta ce an sako ma'aikatata da aka soce

Abdourahamane Hassane
March 31, 2022

Kungiyar Medicin sans frontiere (MSF)  ko Doctors Without Borders ta ce an sako wasu ma’aikatanta guda biyar.

https://p.dw.com/p/49I3r
Symbolbild I 'Medecins Sans Frontieres'
Hoto: Patrick Bernard/abaca/picture alliance

Kungiyar Medicin sans frontiere (MSF) ko Doctors Without Borders ta ce an sako wasu ma’aikatanta guda biyar. Wadanda wasu mutane dauke da makamai suka yi garkuwa da su kusan wata guida a Najeriya. An soce mutanen aka yi garkuwa da su tun cikin watan Faibrairun da ya wuce a garin Fotokol da ke kusa da kan iyakar Najeriya da Kamaru, yankin da kungiyoyin jihadi na Boko Haram da ISWAP ke kai hare-hare. Mutanen guda biyar dake aiki a kungiyar ta Medecin sans Frontiere sun hada da 'yan Chadi da Kamaru da Cote d'Ivoire da kuma Senegal. Sai dai kungiyar ba ta bayyana yadda aka sako wadannan mutane ba, ko an biya kudin fansa ne ko kuma an kubtar da su.