An sako dalibai 79 da aka sace daga wata makaranta
November 7, 2018Talla
Minisitan yada labarai na kasar Kamaru, Issa Bakary Tchiroma, ya ce an sako 'yan makaranta nan saba'in da tara da wasu 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a shekaranjiya Litinin. Ministan dai bai yi wani karin bayani kan hanyoyin da gwamnati ta bi kafin a dawo da yaran ba. Sai dai ya ce har yanzu basu da labari kan malaman da aka yi garkuwa da su tare da wadannan yaran.
Wasu da ake zargin 'yan aware masu fafutukar ballewar daga Kamaru, su suka diran ma makarantar sakandaren da ke a yankin Bamenda, inda suka yi awon gaba da daliban tare da malaman nasu. Wannan shi ne karon farko da kasar mai fama da rikicin masu neman an ballen, ke fuskanta wannan matsala ta yin garkuwa da 'yan makaranta.