1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru: An hallaka 'yan sanda a yankin Inglishi

Gazali Abdou Tasawa
July 10, 2018

Rahotanni daga kasar Kamaru na cewa kimanin 'yan sanda biyu sun hallaka a birnin Buea babban birnin yankin masu amfani da Turancin Ingilishi na kudu maso yammacin kasar.

https://p.dw.com/p/319HX
Kamerun Sprachenstreit Englisch
Hoto: Getty Images/AFP

'Yan sandan sun mutu ne a lokacin wata musayar wuta da wasu masu dauke da makamai. Wani daga cikin jagorin al'umma na birnin na Buea ya tabbatar wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP da mutuwar 'yan sandan biyu. 

Sai dai wata majiyar kiwon lafiya daga birnin na Buea ta ce 'yan sanda biyar da kuma wani fararn hula daya ne  suka halaka a cikin lamari a yayin da wani farar hular na daban ya ji rauni. 

A ranar Lahadin da ta gabata ma dai wasu 'yan bindigar sun bindige wani kwamishinan 'yan sanda a gidansa da ke a garin Kumba da ke tsakanin birnin na Buea da Mamfe. Bayanan da ke fitowa daga yankin na Buea na cewa birnin na cikin tashin hankali inda ko a safiyar wannan Talata aka sake jin karan bindigogi.