Kalubalen taron AU | Siyasa | DW | 15.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kalubalen taron AU

Rikice-rikice a Sudan ta Kudu da Somaliya da kuma Burundi da ma matsayin kassshen Afirka game da kotun kasa da kasa sune abinda zai mamaye taron kolin shugabannin kasashen Afirka.

Sai dai bayaga matsalolin tsaro, batun shugabancin hukumar kungiyar AU, shi ma zai daukar hankali a taron kolin da za a fara ranar Lahadi a birnin Kigali na kasar Ruwanda. Kama aikinta a mukamin shugabar hukumar kungiyar Tarayyar Afirka ta AU, shugabar mai barin gado Nkosazana Dlamini-Zuma ya fara ne da takaddama. Sai dai da aka kai zagaye na hudu kafin ta samu rinjayen kashi biyu bisa uku na yawan kuri'un da take bukata. 'Yar kasar Afirka ta Kudun da ta taba aiki karkashin gwamnatoci uku kuma ta rike mukaman minista guda uku ba ta burge kasashen Afirka da ke magana da harshen Faransanci, abin da har yanzu ke ci gaba da rarraba kan kasashen kungiyar ta AU. To sai dai a cewar Liesl Louw-Vaudran masaniya kan kungiyar ta AU da ke birnin Pretoria na Afirka ta Kudu, Dlamini-Zuma ta taka rawar gani a matsayin shugabar hukumar AU.

Ta ce: "Ko da yake ta sha wahala wajen shawo kan kasashen da suka yi mata rowar kuri'u, amma gaba daya Dlamini-Zuma mace ce mai jajircewa da ta aiwatar da muhimman canje-canje a cikin kungiyar kamar yadda ta yi lokacin da take minista a Afirka ta Kudu kamar a fannin 'yancin mata da jinsi. Saboda haka ina iya cewa ta yi kyakkyawan shugabanci."

Bayan shekaru hudu a bana wa'adin shugabancin Dlamini-Zuma zai kare kuma ta ce ba za ta nemi yin tazarce ba. Saboda haka saben wanda zai gaje ta yana kan jadawalin taron kolin kungiyar AU a Kigali babban birnin kasar Ruwanda, kuma bisa ga dukkan alamu a wanna karon ma za a fuskanci kalubale kamar a shekarar 2012. Masu neman mukamin sun hada da ministar harkokin wajen Botswana, Pelonomi Venson-Moitoi da tsohuwar mataimakiyar shugaban Yuganda, Specioza Kazibwe da kuma ministan harkokin wajen Equirorial-Guinea, Agapito Mba Mokuy. Sai dai dukkansu ukun ba bu mai wani karsashi da zai iya ba wa AU sabuwar alkibla, inji LieslLouw-Vaudran masaniyar AU.Ta ce: "Da yawa daga cikin 'yan AU na masu ra'ayin cewa dole ne a sake bude fagen neman 'yan takara domin dukkan 'yan takarar su uku ba mai kwarewar da ake bukata daga mai son wannan mukamin."

A saboda haka ne aka ba da sunan ministan harkokin wajen Aljeriya Ramtane Lamamra wanda a lokacin da yake matsayin kwamishian majalisar tabbatar da zaman lafiya da tsaro ta AU ya taka rawar gani. Sai dai ksancewa za a ba wa dan kasarsa Smail Chergui shugabancin wannan majalisa a taron kolin an Kigali, ba a wanda zai goyi bayan ba wa 'yan Alajeriya muhimman guda biyu.

Rikice-rikicen da wasu kasashen nahiyar ke fuskanta da kuma batun janyewar nahiyar Afirka daga kotun kasa da kasa za su dauki hankali a taron. Ko da yake maim masaukin baki shugaban Ruwanda Paul Kagame na daga cikin magoya bayan ficewar Afirka daga kotun kasa da kasa amma ba zai fitoa hukumance ya yi maganar a gun taron ba inji Yann Bedzigui na cibiyar nazarin harkokin tsaro .

Ya ce: "Shugabar hukumar AU da kuma shugaban kungiyar ta Tarayyar Afirka Idriss Deby za su zayyana ajandar taron, saboda haka Kagame ba zai iya yin gaban kanshi ba."

Batun janye bisa ga 'yan kasashen AU da ke tafiye-tafiye a nahiyar da ake son ya fara aiki daga shekarar 2018 shi ma za a tattauna kai.

Sauti da bidiyo akan labarin