1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalubale kan isar da kayan agaji Siriya

Ramatu Garba Baba
March 1, 2018

Zarge-zarge tsakanin Rasha da wasu kawayenta kan wargajewar yarjejeniyar tsagaita wuta a Siriya bayan da motocin da ke dauke da kayyakin agaji suka gagara shiga garin Ghouta don isar da kayyayaki ga mabukata.

https://p.dw.com/p/2tUcB
Syrien Damaskus Convoy des Roten Kreuzes fährt nach Madaya und Zabadani
Hoto: Getty Images/AFP/L. Beshara

Motocin Majalisar Dinkin Duniya dauke da tulin abinci da magunguna sun kasa samun damar shiga don sauke kayyakin masarufin a sanadiyar barin wutan da ake ci gaba da yi duk da cewa an cimma yarjejeniya na tsagaita bude wuta a yankin gabashin Ghouta da ke ci gaba da kasancewa a karkashin ikon 'yan tawaye masu adawa da gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad.

Kwanaki hudu kenan da cimma yarjejeniyar bayan wani zama da aka yi da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, inda Rasha ta amince ta dakatar da kai hari na tsawon wata guda, lamarin da ake ganin ya zama dole kafin a iya kwashe marasa lafiya dama wasu da suka sami rauni. Wani babban jami'i a hukumar bayar da agajin Mark Lowcock ya nemi mambobin majalisar da su yi duk mai yi yiwuwa don ganin a mutunta dokar.