Kai dauki ga rayuka a Kahon Afirka | Siyasa | DW | 11.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kai dauki ga rayuka a Kahon Afirka

Matsalar karancin abinci a Somaliland da Puntland na karuwa, inda mutane kimanin miliyan 20 a yankin ke fuskantar barazanar matsananciyar yunwa. Wannan ya kawo taro a Birtaniya.

A babban taron kasa da kasa na tallafa wa Somaliya da kasar Birtaniya ke karbar bakoncinsa a wannan Alhamis za a mayar da hankali kan tara kudaden taimako ga yankin gaba daya.

A garin Dilla da ke yammacin kasar Somaliland ana fama da matsanancin karancin ruwan sha da abinci da magunguna ga mutane da dabbobi abin da kuma a cewa Ahmed Hurre Diiriye da ke zama shugaban kwamitin da ke sa ido kan matsalar fari, idan ba a kai daukin gaggawa ba yawan mutanen da za su mutu zai karu.

Sahra Hawadle Haji 'yar shekaru 45 da haihuwa na daga cikin makiyaya da suka rasa dabbobinsu sakamakon rashin ruwa da abinci.

Somalia Weihwälder in Somaliland (picture-alliance/AP Photo/hotabe)

Dukiya ta tafi dabbobi sun mutu

"Kimanin watanni biyar da suka wuce da ni da iyali da ma dabbobin na muka gudu daga gabashin yankin inda fari ya yi muni zuwa nan wurin. A lokacin dabbobi na sun kai 500, amma yanzu 30 suka saura."

Somaliland na daga cikin yankunan da ke fama da matsalar yunwa a yankin Kahon Afirka. A 1991 yankin da ya ta zaba karkashin mulkin mallakar Birtaniya, ya ayyana 'yancin kansa daga kasar Somaliya, sai dai har yanzu ba ta samun amincewar kasashen duniya ba. Somaliland ta dogara kan kudaden da take samu daga 'ya'yanta da ke ketare, kuma rashin kudaden daga ketare ka iya kara munin bala'in yunwar.

Tun da dadewa masana suka hango matsalar yunwa inji Raheel Chaudhary shi ne daraktan kungiyar agaji ta Care a kasar.

"Tun a watannin Satumba da Oktoba na 2016 ya fito mana cewa karo na uku a jere damina ba za ta fadi ba. Ga da yawa a cikinmu fari ba bakon abu ba ne a Somalia, amma a watan Janerun wannan shekara ya bayyana a fili irin tasirin da rashin ruwan saman zai yi. Kowane mutum daya cikin biyu a Somalia na fama da matalsar yunwa sun kuma dogara kan taimako."

Horn von Afrika Dürre | verendete Ziegen in Somaliland (Arndt Peltner)

Dabbobi da dama sun mutu saboda fari

A birnin Hargeisa da ke zama hedkwatar yankin yunwa ta fara kunno kai. A cibiyar kiwon lafiya a birnin mata da yara suka yi cincirindo suna jiran jami'an kiwon lafiya. A kullum ana samun karin mata da ke zuwa cibiyar dauke da yara masu fama da cututtuka masu nasaba da rashin isasshen abinci. Su ma mata masu juna biyu da ke zwua cibiyar kiwon lafiyar suna fama da karancin abinci. Ana ba wa yaran bisket mai dauke da muhimman sinadarn gina jiki, amma ba su wadatarwa.

Haka ma matsalar ta ke a yankin Puntland wanda a 1998 ya balle daga Somaliya. Abdi Hassin na zama shugaban al'umma a wani gari da ke yankin.

"Mutane na zuwa nan neman taimako na gajere ko dogon lokaci. Sun rasa dukkan dabbobinsu, rayuwa a nan din ma ta yi tsanani. Ya kamata duniya ta taimake mu. Matsalar ta yi muni."

A ilahirin yankin Kahon Afirka dai duk inda ka bi za ka ga matattun dabbobi. Kuma kusan dukkan yara kanana da ke yankunan karkara a yankin suna fama da tamowa. Sai da taimakon kasashen duniya za a iya tinkarar wannan matsala ta yunwa a Somalia da kewaye.

Sauti da bidiyo akan labarin