Kafa dokar ta baci a wasu yankunan Masar | Labarai | DW | 28.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kafa dokar ta baci a wasu yankunan Masar

Bayan barkewar kazamin fadan da ya lamshe rayukan mutane da dama, shugaba Mohammed Mursi ya ayyana dokar ta baci a jihohi uku da ke yankin mashigin ruwan Suez.

Jihohin da dokar ta baci ya shafa sun hada ne da Port Said da Ismailiya da kuma Suez . A cikin jawabin da ya yi ta gidan telebijan shugaban Mursi na Masar ya ce wannan doka za ta rinka aiki ne daga karfe 12 na dare. Kana dokar ta hana fita daga karfe tara na dare zuwa karfe shida na safe, kuma za a shafe kwanaki 30 ana aiki da ita. Mursi ya ce dalilin daukar wannan mataki shi ne bukatar daukar tsauraran matakai na tsaro a daidai lokacin da kasa ta fada cikin wani hali mai hadari.

Akalla mutane 51 suka mutu a cikin aragamar da ta barke a ranar juma'a bayan da aka yanke wa magoya bayan kungiyar kwallon kafar AlMasri na birnin Port Said su 21 hukuncin kisa bisa zargin su da aka yi cewa su ne suka ka ta da fitina bayan wani wasan kwallon kafa da aka yi tsakanin Al-Masri da Al-Ahli a ranar daya ga watan Fabarairun shekarar 2012. Mutane 74 suka muu a cikin wannan artabun.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe