Kaduna: Wani matashin ya kirkiro gilashin gani na makahi | Himma dai Matasa | DW | 14.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Kaduna: Wani matashin ya kirkiro gilashin gani na makahi

Wani matashi a jami'ar Ahmadu Bello Zaria a Kadunan Najeriya ya kirkiro wani gilashi da idan makaho ya sa zai rinka sanar da makaho abin da ke a gabansa.

Wannan tsohon hoto ne da muka yi amfani da shi na wani makahon

Wannan tsohon hoto ne da muka yi amfani da shi na wani makahon

Gilashin da aka sanyawa suna iglass an gabatar da shi a wajen wata gasar fasaha a Najeriya, inda ya ciwo gasar har da kyuatar kudi. Kuma ga duk wanda ya kalli wannan gilashi zai iya cewa karamar magana ce ta zama babba domin daga tattauna batun a dandali hira kamar wasa Mustapha ya ci gaba da ririta fasahar har kawo yanzu ta zama gaskiya. Sai dai saboda yadda gilashin ya hada na'urori dabam-dabam matashin ya nemi agaji daga wasu 'yan uwansa dalibai wadanda su kuma suka kara wa gilashin wasu na'urori ciki har da shigar da makaho yanar gizo.