Kaduna: Matashi ya kirkiro na’urar “E-Xam“ | Himma dai Matasa | DW | 24.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Kaduna: Matashi ya kirkiro na’urar “E-Xam“

A cikin wannan na‘ura ake rubuta jarabawa maimakon rubutawa a takarda kuma nan take za ta bayyanawa dalibi ko yaci wannan jarabawa ko bai ci ba.

Dalibai wadanda rubutunsu ba shi da kyau da malamai masu son gyaran jarabawa a saukake sune suka fi yin murna da wannan fasaha ta matashi Abdulkadir Babagana Musa wanda a yanzu yake ajin karshe na kammala digiri a Jami’ar Ahmadu Bello Zaria.

Babagana dai mai shekaru 25 matashi ne da ya taso da fasaha tun kafin ma ya shiga jamia. Ya ce ya kirkiro wasu na’urori da yawa a baya. A don haka kirkirar wannan na’ura ba ta zo masa da wahala ba.

Jami’ar Maiduguri itace ta fara amfani da basirar wannan matashi, inda dalibai ke cewa fashar Babagana ta kawar da zargin magudi wajen gyaran jarabawa.

A yanzu dai fatan Abdulkadir Babagana Musa shi ne sauran jami’o’in Najeriya su bukaci fara amfani da irin wannan fasaha

 

Sauti da bidiyo akan labarin