Kade-kade da wakoki don dogaro da kai | Himma dai Matasa | DW | 10.04.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Kade-kade da wakoki don dogaro da kai

Wani matashi a Abuja bayan kammala makaranta ya shiga sana'ar sayar da waka da raye-raye a inda yake wakar daurin aure da ta 'yan siyasa domin dogaro da kai har da ta kai ga kafa kamfani nasa.

YouTube - Roboterhand der Cambridge University spielt Klavier (YouTube/Cambridge University)

Piano daya ne daga cikin kayan kida na zamani kamar wannan a jami'ar Cambridge

Tun dai a shekara ta 2009 ne matashi Ismail Muhammed Jada da ke zaune a Abuja babban birnin Najeriya wanda ya kammala karatunsa mai zurfi ya fara sana'ar rubuta waka da rerawa da halartar tarurruka da suka hada da na suna da daurin aure don rera waka ta yadda a sakamakon hakan yake samun kudaden shiga domin harkokin yau da kullum a maimakon ya shiga aikin gwamnati.

Duk da cewa matashi Ismail Muhammed ya dan sami tirjiya daga mahaifansa kan sana'ar waka don ya sayar da ita to amma daga baya suka goya masa baya a inda yanzu haka yake da tarin matasa da ke amfana da wannan sana'ar da amfaninta ke zama ilimantarwa da nishadantarwa. A wannan sana'a ya samu abin hawa da siyan fili da ma daukar nauyin yara zuwa makaranta.

Kowacce irin sana'a dai na cin karo da kalubale a inda itama sana'ar rubuta waka ke fuskantar matsaloli kamar dai yadda Ismail Muhammed Jada ya shaida wa tashar DW fahimtar da magabata su fahimci manufar sana'ar babban lamari ne.

Dini Mai sa'a mawaki ne da suke tare da Ismail Jada ya ce shakka babu al'umma da dama a wannan karnin sun yi wa mawaka mummunar fahimta to amma sannu a hankali yanzu haka an fara ganewa.

Tuni dai Ismail Muhammed Jada ya assasa kamfani nasa mai zaman kansa mai suna Abuja Multi Media Studio ya ce babban burinsa shi ne matasa su gane mahimmacin kama sana'a maimakon dogaro da aikin gwamnati ta yadda za su iya dogaro da kansu.

Sauti da bidiyo akan labarin