Jirgin yakin Faransa ya Kai hari akan IS | Labarai | DW | 01.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jirgin yakin Faransa ya Kai hari akan IS

A yau ne jiragen yakin kasar Faransa suka kai wani hari a kan wasu bututun man kungiyar mayakan IS kusa da birnin Raqa da ke a Syriya.

Harin na jiragen dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ministan tsaron Faransa ya kai ziyara sansanin jiragen yakin Faransa dake a Jordan inda jiragen suka kai harin.Minisatan tsaron Jaean Le Drian yace an sanar damu batun kai harin da aka kai cikin dare kuma ya kamata mu ci gaba da daukar matakai irin wadan nan domin dakile ayyukan mayakan IS.

Wannan dai shi ne hari na farko a cikin wannan shekarar da Faransa ta kai a kan mayakan IS ata cewar wata majiya daga yawun rundunar sojojin kasar Faransa.