1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaThailand

Jirgin Singapore Airlines ya yi saukar gaggawa a Bangkok

Abdourahamane Hassane
May 22, 2024

irgin kamfanin jiragen sama na Singapore Air, ya yi saukar gagawa a birnin Bangkok na Thailand a sakamakon cikas da ya samu bayan ya tashi daga birnin London.

https://p.dw.com/p/4g9N2
Hoto: Markus Mainka/picture alliance

 FasinjanJirgin samfarin SQ321 sun gamu da mummunan tashin hankali a kololuwar sarararin samaniyar kasar Myanmar inda jirgin ya rika yin tanga-tangal. A cewar wani fasinja, mutane dake zaune a kujerun baya, sun gangaro gaba,a tsiyace suna buguwa da juna, da yawa dai  sun jikkata har mutum daya ya mutu. yayin da aka kwantar da wasu mutanen 20 a asibiti. Hotunan da aka dauka a cikin jirgin,samfarin Boeing kirar, Amurka ya nuna jakukukan kaya da kwalabe da abinci da ke rataye saman rufin jirgin duk sun zubo kasa.