1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tangardar Jirgin Singapore Airlines

May 21, 2024

Mutum daya ya rasa ransa wasu fiye da 70 kuma sun sami raunuka bayan da jirgin fasinja na Singapore Airlines ya fuskanci tangardar iska mai karfi yayin da yake tafiya a sararin samaniya.

https://p.dw.com/p/4g7dd
Jirgin Singapore Airlines
Jirgin Singapore AirlinesHoto: Pongsakornr Rodphai/Handout/REUTERS

Bayan daidaituwar al'amura jirgin ya yi saukar gaggawa a Bangkok a cewar wata sanarwa da kamfanin jirgin ya fitar.

Wani dan Burtaniya mai shekaru 73 da haihuwa ya rasu a lamarin a sakamakon abin da ake kyautata zato bugun zuciya ne kamar yadda daraktan kamfanin jirgin ya shaida wa yan Jarida. Wasu mutanen da dama sun sami raunuka a ka.

Jirgin kirar Boeing 777-300 na dauke da fasinjoji 211 da ma'aikata 18.