Jirgin saman dakon kaya ya fadi a Sudan ta Kudu | Labarai | DW | 04.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jirgin saman dakon kaya ya fadi a Sudan ta Kudu

Mutane da dama sun hallaka sakamakon hadarin jirgin sama na dakon kaya Sudan ta Kudu wanda ya fadi a kan hanyar zuwa arewacin kasar.

Rahotanni daga kasar Sudan ta Kudu sun nuna cewa fiye da mutane 20 sun hallaka lokacin da jirgin saman dakon kaya da ya tashi daga birnin Juba fadar gwamnatin kasar ya fadi. Jirgin saman ya fadi a kan hanyar zuwa Jihar Upper Nile da ke yankin arewacin kasar, kamar yadda mai magana da yawun shugaban kasar ya tabbatar.

Jirgin saman ya fadi a cikin dajin da kogin Nilo ya ratsa. Kawo yanzu ana ci gaba da tattara bayanai kan hakikanin abin da ya faru.