1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iraki: Jirgin ruwa ya kashe sama da mutane 70

Yusuf Bala Nayaya
March 21, 2019

Wadanda suka mutu mafiya yawa mata ne da kananan yara wadanda ke halartar bikin Nowruz da ke zuwa a farkon shekarar ta Kurdawa da farkon bazara.

https://p.dw.com/p/3FRw2
Irak Fährunglück bei Mossul
Hoto: Reuters

Sama da mutane 70 ne suka rasu bayan da wani jirgin ruwa makare da jama'a ya kife a lokacin da ake bikin sabuwar shekarar Kurdawa a kogin Tigris a kusa da iyakar birnin Mosul. Mafi yawa mutanen da suka rasu mata ne da yara kamar yadda jami'ai suka bayyana.

Kanal Hussam Khalil, shugaban jami'an tsaro na farin kaya a lardin arewacin Nineveh ya fada wa kamfanin dillancin labaran AP cewa wadanda suka mutu mafiya yawa mata ne da kananan yara wadanda ke halartar bikin Nowruz da ke zuwa a farkon shekarar ta Kurdawa da farkon bazara. Daruruwan mutane ne dai ke cikin jirgin kafin kifewar tasa. Mata da kananan yara suka fi yawa cikin mamatan.