Iraki: Jirgin ruwa ya kashe sama da mutane 70
March 21, 2019Talla
Sama da mutane 70 ne suka rasu bayan da wani jirgin ruwa makare da jama'a ya kife a lokacin da ake bikin sabuwar shekarar Kurdawa a kogin Tigris a kusa da iyakar birnin Mosul. Mafi yawa mutanen da suka rasu mata ne da yara kamar yadda jami'ai suka bayyana.
Kanal Hussam Khalil, shugaban jami'an tsaro na farin kaya a lardin arewacin Nineveh ya fada wa kamfanin dillancin labaran AP cewa wadanda suka mutu mafiya yawa mata ne da kananan yara wadanda ke halartar bikin Nowruz da ke zuwa a farkon shekarar ta Kurdawa da farkon bazara. Daruruwan mutane ne dai ke cikin jirgin kafin kifewar tasa. Mata da kananan yara suka fi yawa cikin mamatan.