1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jirgin Sabiya ya fadi a kasar Girka

Abdoulaye Mamane Amadou
July 17, 2022

Mutane takwas sun mutu a hadarin jirgin dakon kaya na kasar Sabiya mallakar wani kamfanin a lardin Kavalas mai tsaunuka na arerwacin Girka.

https://p.dw.com/p/4EFxK
Griechenland | Flugzeugabsturz in Kavala
Hoto: Giannis Papanikos/AP Photo/picture alliance

Makare da makamai da suka kai nauyin ton 11 jirgin saman wanda ke kan hanyarsa ta zuwa Bangladesh, ya fadi ne a lardin Paleochori Kavalas mai tsaunuka jim kadan bayan tashinsa, kuma daukacin ma'aikatan jirgin su takwas wadanda dukkaninsu 'yan kasar Ukraine ne sun mutu a cewar ministan tsaron Sabiya Nebojsa Stefanovic a yayin wani taron manema labarai,

Ministan ya kara da cewa"Jirgin ya tashi ne daga birnin Nis da misalin karfe takwas da minti 40 na dare, dauke da makaman da ma'aikatar tsaron Bangladesh ta siya daga kamfanin Valir, an tsara jirgin zai isa Dakah bayan ya yada zango a Amman da Riyad."

Sabiya ta karyata jita-jitar da aka rika yadawa cewa makaman za a kaisu ne kasar Ukraine wacce ke gwabza yaki da Rasha.