Jiran tsammani kan sasanta Ukraine | Labarai | DW | 12.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jiran tsammani kan sasanta Ukraine

An fara ganin alamar cimma wani abun azo a gani a taron sasanta rikicin kasar UKraine wanda aka fara tun jiya Laraba a birnin Minsk na kasar Belarus

Rahotanni dake fitowa daga Minsk inda shugabanni ke ganawar, na nuna cewa nan bada jimawa za a saka wa wata yarjejeniya hannu, da ake fatan za ta kai ga kawo karshen rikicin da aka yi watanni goma ana fama da shi. Taron wanda ya samu halartan shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, shugaban kasar Ukraine Petro Proshenko da takwaransa na FaransaFrançois Hollande, dama wakilan 'yan aware da ke neman balle daga kasar ta Ukraine, an gira shi ne domin a kawo karshen zubar da jini, inda fada ke kara yin kamari tsakanin sojan gwamnatin Ukraine mai ra'ayin kasashen Yamma da 'yan aware masu dasawa da Rasha. Wata majiya ta ce mahalarta taron sun bukaci a tabbatar da yin aiki da yarjejeniyar da aka cimma a watan Satumban bara.