Jiran sakamakon zaɓenshugaban ƙasa a Sierra Leone
September 11, 2007Talla
Al´ummomin ƙasar Sierrra Leone, na ci gaba da jiran sakamakon zaɓen shugaban ƙasa zagaye na 2, wanda a ka gudanar a ƙarshen mako.
Ya zuwa yanzu hukumar zaɓe mai kanta, ba ta fito hili ba, ta bayyana ɗan takara da ya lashe wannan zaɓe, to saidai Ernest Bai Koroma, na jam´iyar adawa yayi iƙirarin samin gagaramin rinjaye.
Daga cikin kashi 1 bisa 5 na runfunan zaɓen da a ka tattara sakamakon su, Ernest Bai Koroma, ya sami kashi 64 cikin ɗari na jimmilar ƙuri´un da aka kaɗa.
Kakakin jam´iyar SLPP mai riƙe da ragamar mulki, Victor Reider, ya zargi ɗan takara Bai Koroma, da riga malam massalaci, a game da sakamakon wannan zaɓe.