Jiragen yaki sun kashe mutane 20 a Yemen | Labarai | DW | 19.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jiragen yaki sun kashe mutane 20 a Yemen

Akalla mutane 20 ne suka mutu yayin da jiragen suka kai hari a yankin Taiz, hukumar kula da 'yan kudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce harin ya ritsa da wasu iyalai da ke gudun hijira.

Hukumomi sun ce wannan harin ya shafi jami'an tsaro da ke sintirin kare fararen hula da ke neman tserewa yankunan yaki a kasar. A yanzu dai sama da mutane dubu 200 ne suka rabu da gidajen su sakamakon tsananin tashin hankula sakanin 'yan tawaye dake jan daga da bangaren gwamnati.

Sama da shekaru hudu kenan kasar Yemen ke fama da tashin-tashina tsakanin shugaba Abd Rabu Mansour Hadi da 'yan tawayen Huthi, amma abin ya fi tsnanta ne a shekara ta 2015 lokacin da 'yan tawayen Huthi suka samu galaba na mamaye kudancin kasar Yemen.