Jiragen sama sun soma tashi daga London | Labarai | DW | 28.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jiragen sama sun soma tashi daga London

Kamfanin jiragen saman na British Airways ya sanar da soma tashin jiragensa a wannan Lahadin daga birnin London, da kuma daidaituwar lamurran wasu filayen jiragen saman kasar da aka fuskanci matsalar na'ura.

British Airways Flugzeug (picture-alliance/empics)

Jiragen kamfanin British Airways na Britaniya.

Sanarwar British Airways tta ce za a ci gaba da fuskaatar tangarda, bayan da matsalar na'urar da ke tsara ayyukan filayen jiragen saman ta kai ga dakatar da tashin dukannin jirage daga birnin London a ranar Asabar. Kuma sanarwar ta ce a halin yanzu sai wanda ya riga ya sayi tikiti wanda kuma ya samun tabbacin cewa an amince da tikitinsa ne zai iya zuwa a filayen jiragen sama guda biyu, sannan ya sake tantancewa a wurin.

A cikin wani sako na bidiyo da ya wallafa ta shafinsa na Twitter babban Dakectan kamfanin na British Airways Alex Cruz, ya ce matsalar ta samo asali ne daga wata na'ura da ke samar da wutar lantarki, kuma abun bashi da nasaba da wani kutse na masu kai hari ta Internet.