Jerin tashin bama-bamai a Abuja | Labarai | DW | 03.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jerin tashin bama-bamai a Abuja

Akalla mutane 15 suka mutu wasu kimanin 40 suka jikkata bayan tashin bama-bamai a Kuje da Nyanya, wadanda anguwanni ne a babban birnin Tarayyar Najeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa bama–bamai biyu ne suka tashi a cikin garin Kuje, shelkwatar karamar hukumar Kuje a babban birnin Tarayyar Najeriya. Alhaji Shuaibu Mai Tifa mazaunin Kuje ya yi wa DW karin bayani, inda ya ce hari daya an kai shi ne a harabar ofishin 'yan sanda, yayin da daya harin aka kai shi a kasuwar garin wanda kuma wata mahadar hanya ce da ke da cunkoson jama’a. Ana tsoron mutane da dama sun mutu a harin.

A anguwar Nyanya ma wani bam din ya tashi, inda ya fashe a karkashin wata gada da aka taba tada wani bam din a Abuja. An fuskanci fashewar bama-baman ne kwana guda bayan bikin cikar Najeriya shekaru 55 da samun ‘yancinta. Kuma kusan mazauna a Abuja har sun saki jiki sun manta da ganin irin wannan tarzoma sama da shekara guda.