Jawabin Gordon Brown na farko tun da ya zama Firministan Birtaniya | Labarai | DW | 24.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jawabin Gordon Brown na farko tun da ya zama Firministan Birtaniya

FM Birtaniya Gordon Brown ya gabatar da jawabinsa na farko a matsayin shugaban jam´iyar Labour a gun babban taron ta na shekara shekara. Brown wanda ya hau kan kujerar FM Birtaniya kimanin watanni 3 da suka wuce ya ce zai dora Birtaniya akan wata sabuwar turba don dacewa da bukatun ´yan kasar tare da ba su karfin yin gogayya da takwarorinsu na duniya. An dai yada jita-jitar cewa Brown zai yi amfani da jawabin don sanar da shirya zabe na gaba da wa´adi to amma bai ce komai a dangane da wani zabe ba. Maimakon haka FM ya lashi takobin sa kafar wando guda ne da masu tsattsauran ra´ayin addini. Ya kuma yi kira ga gwamnatin Sudan da ta girmama hakin mata da yara musamman a lardin Darfur.

Brown ya ce “Sakon mu kai tsaye ga gwamnatin Sudan shi ne dole ta daina keta hakkin bil Adama ko kuma ta fuskanci tsauraran takunkumai. Ba zamu saduda har sai an kawo karshen yin ruwan bama-bamai, a tsagita wuta sannan a warware rikicin.”