1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Togo ya dauki hankulan jaridun Jamus

Mohammad Nasiru Awal RGB
December 21, 2018

Jaridun Jamus sun yi sharhi kan zaben 'yan majalisar dokokin kasar Togo da aka gudanar a ranar Alhamis da ta gabata.

https://p.dw.com/p/3AUVH
Togo Wahl | Wahllokal in Lome
Hoto: Getty Images/AFP/M.F. Koffi

Zaben 'yan majalisar dokokin Togo zai kara wa jam'iyyar da ke mulki karfi bayan kaurace wa zaben da 'yan adawa suka yi. Matukar jam'iyyar gwamnati ta samu kashi hudu cikin biyar na yawan kujeru casa'in da daya a majalisar to za ta iya a nan gaba ita kadai ta yanke shawara kan muhimman canje-canje har izuwa da kwaskware kundin tsarin mulki. Da haka Shugaba Faure Gnassingbe, wanda tun a shekara ta 2005 ya ke kan shugabantar kasar, ka iya darewa kan karagar mulki bayan zaben 2020. Yanzu haka dai Shugaba Gnassingbe ya fi kowane shugaban kasa a Afirka ta Yamma dadewa kan mulki. Kawancen jami'iyyun adawa goma sha hudu a kasar ta Togo suka kaurace wa zaben majalisar dokokin na ranar Alhamis suna musu yin tir da tsarin shugabancin kasar da ya zama tamkar na gado. Mahaifin shugaban marigayi Gnassingbe Eyadema ya mulki kasar tsawon shekaru 38.

Idan muka leka makwabciyar Togon wato kasar Ghana, masana ilimin fasahar dagital suka yi wani taro na yini biyu karkashin taken "Next Level" wato mataki na gaba, a birnin Accra, kamar yadda jaridar Berliner Zeitung ta labarto. Ta ce a babban taron farko na kungiyar republica a birnin Accra, masana fasahar digital dubu biyu ne suka duba damarmaki na hadakar intanet tsakanin kasa da kasa. An duba batutuwa na sabbin fasahohi a intanet da kare bayanai ta yanar gizo da 'yancin al'umma kan intanet. Ganin yadda taron ya yi nasara kungiyar tarayyar Afirka ta alkawarta sake shirya taron a shekara mai zuwa.

Ita kuwa jaridar Franfurter Allgemeine Zeitung tsokaci ta yi kan taron koli tsakanin tarayyar Turai EU da takwararta ta Afirka AU da ya gudana a birnin Vienna na kasar Ostiriya a ranar Talata. An shirya taron ne don karfafa gwiwar kamfanonin Turai su kara yawan jarin da suke zubawa a Afirka, musamman a fannin fasahar digital da kirkire-kirkire, amma daga baya batun bakin haure ya mamaye zauren tattaunawar. EU ta yi wa Afirka alkawari na saka hannun jari a bangarori da dama domin a cewarta makomar Turai ta dogara da makomar Afirka, bai kuma kamata Turan ta ja baya ta bari wasu kasashe kamar China su yi ta cin karensu babu babbaka a Afirka. Shugaban hukumar tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat ya ce ba daidai ba ne kasashen duniya su mayar da nahiyar Afirka tamkar wani fagen gogayya da juna.

A karshe sai jaridar Süddeutsche Zeitung wadda a labarinta mai taken kayayyakin kwalliya masu hadari ta ce kasar Ruwanda ta haramta amfani da mayuka da wasu kwayoyi da ke kara hasken fatar jikin dan Adam. Ta ce gwamnati a Ruwanda ta sanya sunayen mayuka da kwayoyi kimanin dubu daya wadanda ta ce suna kunshe da wasu sinadarai masu hadari ga dan Adam da ke amfani da su don canja launin fatar jikinsu. Yanzu haka kuma 'yan sanda sun kwace da yawa daga cikinsu. Ma'aikatar kiwon lafiya ta ce haramcin kadai ba zai wadatar ba dole sai an hada da kamfen na wayar da kan al'umma dangane da hadarin da ke tattare da wadannan mayuka.