1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridu sun dubi zaben Kwango da noma da makamashi a Afirka

Mohammad Nasiru Awal
December 14, 2018

Daga cikin abubuwan da ke daukar hankali a Afirka a yanzu, su ne batun zabe a Kwango, abin da ya sanya batun zama abin nazari tsakanin jaridu. A Jamus ma an dubi batun da sauran wasu kan Afirka.

https://p.dw.com/p/3A6fK
Congolese presidential contender Etienne Tshisekedi
Hoto: DW/S. Mwanamilongo

A daidai lokacin da ya rage kwanaki kalilan gabanin gudanar da zaben shugaban kasa a Kwango, a cewar jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, fargaba na karuwa dangane da samun rigingimu, ko da yake shugaba mai ci Joseph Kabila ba zai tsaya takara ba, amma zai ci gaba da jan zarensa.

Jaridar ta ruwaito dan Kwangon wanda a ranar Litinin da ta gabata da shi da wata matashiya 'yan kasar Iraki suka karbi kyautar zaman lafiya ta Nobel a bana a birnin Oslo na kasar Norway, wato Denis Mukwege na kashedin cewa zaben shugaban kasar Kwango da zai gudana a ranar 23 ga watan nan na Disamba, ka iya jefa kasar cikin sabon yakin basasa saboda rashin yin shirye-shiryen zabe da suka kamata, sabanin haka an fi mayar da hankali kan shirye-shirye na matakan soji.

Mukwege wanda likita ne, ya nuna damuwar cewa ba za a kamanta gaskiya da adalci a zaben ba, ba kuma zai guna cikin kwanciyar hankali da lumana ba, lamarin da zai sa wadanda suke ganin an yi musu magudi su yi fatali da sakamakon zaben.

Verleihung Friedensnobelpreis Denis Mukwege Nadia Murad
Denis Mukwege, likitan kasar Kwango da aka bai wa kyautar NobelHoto: NTB Scanpix/Haakon Mosvold Larsen/Reuters

Har yanzu dai muna a kasar ta Kwango amma a kan kyautar zaman lafiyar da likitan wato Denis Mukwege ya samu, inda jaridar Die Tageszeitung ta ce shi dai likitan mai shekaru 63 wanda ya gina wani asibitin mata a Kwango, ya dukufa wajen ceto tare da yin jinya ga matan da kungiyoyi masu daukar makami a gabashin Kwango suka ci zarafinsu.

 

Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung a wannan makon ta leka kasar Tanzaniya tana mai cewa shugaban kasa John Magufuli da a farkon kama madafun iko ya mayar da hankali wajen yaki da cin hanci da rashawa, yanzu yana daukar matakai a dukkan bangarori na kasar.

A halin da ake ciki shugaban ya tsoma bakinshi a harkar noman kashew daya daga cikin ababan da ke samar wa Tanzaniya kudaden musaya na ketare. Kasancewa farashin kashew ya fadi a kasuwannin duniya, shugaban ya kara farshin kasewa din da kashi 10 cikin 100. Ganin yadda masu sayen kashew a cikin gida suka ki biyan sabon farashin duk da barazanar janye musu lasisi, shugaban ya umarci bankin kasar da ya saye dukkan kashew din da aka girba a wannan shekara. Sai dai bisa ga dukkan alamu shugaban ya dauki wannan mataki ne don samun magoya baya kasancewa manoman kashewa din a yankunan na 'yan suke.

Tanzania President John Pombe Magufuli in Dar es Salaam
Shugaba John Magufuli na kasar TanzaniyaHoto: DW/S. Khamis

Yawan daukewar wuta a Afirka ta Kudu inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tana mai cewa wata badakalar cin hanci a hukumar samar da hasken wutar lantarki ta kasa ta jefa Afirka ta Kudu cikin duhu sakamakon yawan daukewar wutar lantarki, lamarin da ya janyo koma baya ga tattalin arzikin kasa. Matsalar dai na da nasaba da rashin yi wa injunan samar da wutar lantarki gyara na tsawon lokaci. A shekarar 2014 kasar ta fuskanci wannan matsala ta daukewar wutar lantarki.