1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar gwamnatin Najeriya a jaridun Jamus

Lateefa Mustapha Ja'afar RGB
June 2, 2023

Akasarin jaridun Jamus sun yi sharhi kan shagulgulan bikin rantsar da sabon shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.

https://p.dw.com/p/4S7gS
Sabon shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Sabon shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed TinubuHoto: Sunday Aghaeze/AP Photo/picture alliance

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung a sharhinta mai taken: "Da kade-kade da badujala da faretin sojoji aka rantsar da sabon shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu. Sai dai har yanzu, nasararsa na cike da ce-ce-ku-ce. Jaridar ta ce, Najeriya kasa mafi yawan al'umma a Afirka ta yi sabon shugaba. A ranar Litinin da ta gabata, aka rantsar da Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima cikin kasaitaccen biki da faretin sojoji, inda rahotanni suka bayyana cewa, sama da mutane 300 aka gayyata yayin rantsuwar da ta gudana a dandalin Eagle Square da ke Abuja fadar gwamnatin kasar.

Daga cikin manyan bakin da suka halarta, akwai shugabannin kasashen Burundi da Chadi da Jamhuriyar Nijar da Ghana da kuma Afirka ta Kudu, yayin da miliyoyin 'yan Najeriya suka kalla kai tsaye ta akwatunan talabijin. Cikin watan Fabarairun wannan shekara ne dai, aka zabi Tinubu a matsayin shugaban kasa da kuri'u kaso 27 cikin 100 kacal, adadin da ke zaman mafi karanci a tarihin zabukan kasar. Sai dai har yanzu, 'yan takarar manyan jam'iyyun adawar kasar Atiku Abubakar na PDP da kuma Peter Obi na Labour na kalubalantar sakamakon a kotu. Akwai dai tarin kalubale a gaban sabon shugaban kasar, kama daga matsalar tattalin arziki da rikice-rikice da rashin tsaro baya ga dimbin matsalar rashin aikin yi a tsakanin al'ummar kasar.

Janar Abdel Fattah al-Burhan da rundunar gwamnatin Sudan
Janar Abdel Fattah al-Burhan da rundunar gwamnatin SudanHoto: Sudanese Armed Forces/REUTERS

Ita kuwa jaridar die tageszeitung ta rubuta sharhinta ne mai taken: Gwamnatin Sudan ta dakatar da tattaunawar sulhu, Shugaba Abdelfattah al-Burhan ya yi barazanar zafafa yakin da kuma janyewa daga teburin sulhu da sojojin 'yan tawaye na RSF a Saudiyya. An yi zargin an garkame Khartum babban birnin kasar. Yaki tsakanin sojojin gwamnati da na 'yan tawayen RSF a Sudan, na kara kamari. A Larabar wannan makon shugaban kasa kana babban kwamandan askarwan kasar Abdelfattah al-Burhan ya dakatar da tattaunawar tsagaita wutar da ke gudana a Saudiyya, kamar yadda jami'an diplomasiyyar Sudan din da kuma  kafafen yada labarai masu yawa suka tabbatar.

Yunkurin dakile matsalar kwararar bakin haure
Yunkurin dakile matsalar kwararar bakin haureHoto: Reuters/I. Zitouny

Za mu karkare ne da jaridar ta Die Tageszeitung a sharhinta mai taken: Rikicin Libiya na haifar da matsaloli ga masu fasakwauri a kasar. Gwamnati na yin barin bama-bamai a biranen da ke gabar ruwan kasar da jirage marasa matuka. Jaridar ta ce, gwamnatin ta dauki matakin ne da nufin dakile kwararar bakin haure zuwa Tekun Bahar Rum. Sai dai jiragen ruwa na sauya akalarsu zuwa wani bangare na gabar ruwan. Ta ce, a Libiya jirage marasa matuka na yin ruwan bama-bamai  a garuruwan Zawiya da Zuwara da ke gabar ruwa, sai dai hakan ya janyo asarar rayukan kimanin mutane hudu. Jiragen marasa matuka, sun yi barin wuta a babban birnin kasar Tripoli, inda suka kai hari kan mayakan Buzriba. Iyalan ne ke kula da wuraren da ake ajiye firsinonin da ake safararsu zuwa ketare a Zawiya zuwa Tsibirin  Lampedusa.