1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka a Jaridun Jamus: AFCON da corona

Usman Shehu Usman LMJ
January 21, 2022

Rikicin Mali da annobar corona a Afirka da kuma gasar cin kofin kwallon kafar Afirka AFCON, sun dauki hankalin jaridun Jamus a wannan makon.

https://p.dw.com/p/45v6H
Mali | Sgugaban gwamnatin riko ta soja Assimi Goïta
Shugaban kasar Mali Assimi GoïtaHoto: Präsidentschaft der Republik Mali

A sharhin da ta rubuta kan kasar Mali, jaridar Süddeutsche Zeitung ta ce yanzu mako guda kenan gwamnatin Mali ta hana wani jirgin saman sojojin Jamus tashi daga Bamako. Hana jiragen sama zirga-zirgar ya shafi ayyukan dakarun Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Mali, musamman sojojin Jamus da lamarin ya shafa a baya-bayan nan. Ma'aikatar tsaron Jamus ta ce ba a taba samun irin wannan takaddama ba. Gwamnatin Mali dai ta ce gaza yin sahihiyar rijista da ya kamata sojojin Jamus din su yi ne, ya janyo samun tsaikon. Jamus dai na da dakaru kimanin dubu daya da 300 a kasar Mali, wadanda ke aiki karkashin kungiyar Tarayyar Turai EU da kuma Majalisar Dinkin Duniya.

Afirka ta Kudu riga-kafin Covid-19 a Soweto
Yiwuwar samun kamfanin yin alluran riga-kafin corona a Afirka ta KuduHoto: Siphiwe Sibeko/REUTERS

A nata sharhin jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, ta ce Afirka ba ta bukatar sayo alluran riga-kafi da ga wata nahiya. Jaridar ta ce wani kamfanin kasar Amirka ya zuba jari na makudan kudi a kasar Afirka ta Kudu, domin sarrafa magunguna. Wani kwararren likita kana shahararren dan kasuwa Patrick Soon-Shiong dan kasar Afirka ta Kudu da Amirka ke shirin kafa kamfanin da zai sarrafa daukacin alluran riga-kafin da ake bukata a Afirkan.

Kamerun Jaunde | Africa Cup of Nations
Gasar AFCON na ci gaba da gudana a KamaruHoto: Kepseu/Xinhua/imago images

Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung ta rubuta nata sharhin ne kan gasar cin kofin kwallon kafa ta nahiyar Afirka AFCON da ke gudana a yanzu haka a Kamaru. Jaridar ta ce shugaban da ya dade kan mulki Paul Biya na fatan samun kyakkyawan suna sanadiyyar gasar da ake fafatawa a yanzu haka a kasarsa. Shugaban mai shekaru 88 da duniya, kasarsar mai masaukin baki Kamaru ta lashe Burkina Faso da ci biyu da daya. Wannan ya yi wa shugaban dadi, domin kusan abin da ya mamaye gwamnatinsa cikin makwannin nan, shi ne batun wasanni da yanzu haka kasarsa ke karbar bakwanci.