1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cikon shekaru biyu da faduwar gwamnatin Sudan

January 15, 2021

Yoweri Museveni mai shekaru 76 wanda ya kwashe shekaru 35 yana yin mulki na ci gaba da dagewa a kan matsayin shugaban kasa duk da kalubalan da ke fuskanta daga matashi mawaki dan shekaru 38 Bobi Wine.

https://p.dw.com/p/3nyLj
Bildkombo | Yoweri Museveni und Bobi Wine
Daga hagu zuwa dama,Yoweri Museveni tare da Bobi Wine

Jaridar Der Tagesspiegel cewa ta yi shahararren mawaki na kalubalantar tsohon jagoran 'yan tawaye. Jaridar ta ce tun wasu watanni gabanin zaben na shugaban kasar Yoweri Museveni mai shekaru 76, ke kokarin shawo kan matasan kasar cewa har yanzu yana da jini a jika, inda a wuraren yakin neman zabe ya kan cashe tare da wasu mawaka matasa, don rufe bakin babban mai kalubalantarsa wato mawakin nan dan shekara 38, da ya rikide ya zama dan siyasa, Robert Kyagulanyi da ake wa lakabi da Bobi Wine, da ke kan gaba wajen sukar lamirin Shugaba Museveni da ke neman wa'adin mulki karo na shida. Kusan shekaru 35 ke nan Museveni, tsohon dan tawaye, da a da ya yi kaurin suna wajen sukar shugabannin Afirka da suka mayar da mulki sai mutuwa ka raba, ke jan ragamar mulkin kasar ta Yuganda.

Bobi Wine na samun goyon bayan matasa na Yuganda a fafutukar da yake na neman sauyi

Afrika Uganda Wahlen
Hoto: Jerome Delay/AP/picture alliance

Mawakin salon kida rap Bobi Wine yana samun goyon bayan matasan Yuganda ya sha alwashin lashe zaben kasar, amma shugaban kasa na amfani da karfin hatsi don ci gaba da mulki, taken labarin da jaridar Süddeutsche Zeitung ta buga gami da zaben kasar Yuganda. Ta ce dan adawa na fuskantar tursasawa daga hukumomin tsaro, haka ma wasu a cikin magoya bayansa sun rasa rayukansu a hannun 'yan sanda, amma duk da haka matashin bai saduda ba a gwagwarmayar neman sauyi a Yuganda. Ko da yake a da kasashen yamma na ganin Museveni a matsayin tabbaci na zaman lafiya da kwanciyar hankali amma yanzu tursasa wa 'yan adawa ya zama ruwan dare a Yuganda.

Sudan matasa na gargadin cewar idan sojoji suka kankane madafun iko fiye da kima za su tada kayar baya.

Äthiopien I  Sudan I Konflik
Hoto: Mahmoud Hjaj/Anadolu Agency/picture-alliance

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung ta leka kasar Sudan tana mai cewa kusan shekaru biyu ke nan da faduwar gwamnatin shugaban mulkin kama karya Omar al-Bashir, amma har yanzu al'umma a Sudan na jiran samun rayuwa mai inganci. Jaridar ta ce tattalin arzikin kasar ya karye, hauhawar farashin kaya na dada yin muni, har yanzu kuma sauye-sauye a kasar na tafiyar hawainiya. Sai dai wasu daga cikin 'yan kasar na da yakinin cewa al'amura za su inganta, domin a ganinsu har yanzu ba a kawo karshen juyin juya halin ba har sai an kai ga girka gwamnatin farar hula tsantsa. Matasa a kasar, ko da yake ba sa fantsama kan titi don zanga-zanga, amma suna sa ido kan abubuwan da ka je su komo musamman a fagen siyasa, amma suna masu cewa idan sojoji suka kankane madafun iko fiye da kima za su tada kayar baya. Jaridar ta jiyo matasan na cewa a shirye suke su kaddamar da bori shigen wanda ya kifar da gwamnatin da ta shude.

Mutane na yin kaura daga Tigray bayan yakin da aka gwabza

Äthiopien Verteidigungstruppe Amhara
Hoto: Alemnew Mekonnen/DW

A karshe za mu leka makwabciyar Sudan wato Habasha inda a labarin da ta buga jaridar Neues Deutschland ta ce tun bayan da firaministan Habasha Abiy Ahmed ya kaddamar da farmaki kan kungiyar kwatar 'yancin yankin Tigray a watannin karshe na shekarar 2020, fiye da mutane dubu 20 suka tsere dag yankin ba tare da sanin makomarsu ba, yanzu haka suna rayuwa cikin wani mawuyacin hali a wani sansani da ke kasar Sudan. Jaridar ta ce sukurkucewar harkar kiwon lafiya da yanayi na kazanta na zama babban abin damuwa a sansanin.